
3 Fabrairu 2024
Bayan da matarsa da kuma ɗansa suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara, Abubakar Wakala ya fara tunanin fara ɗaukar mataki.
Manomin mai shekara 80 ya fara yaƙi da ba-haya a fili a ƙauyensu na Kinder da ke arewacin Najeriya.
Ya ce : “Da na ga lamarin na neman wuce kima, ana ta kai mutane asibiti, sai na fara gangamin''.
Ƙauyensa na cikin hatsarin ambaliya ruwa, wanda ke ƙara hatsarin kamuwa saboda rashin tsafta.
Ya ce: “Kafin fara gangamin, mutane kan yi ba-haya a ko'ina. Mun kuma fahimci cewa hakan ba daidai ba ne, daga nan sai muka fara bai wa mutane shawara cewa a duk lokacin da za su yi ba-haya su riƙa shiga daji, su kuma tona rami, sannan su binne idan sun kammala''.
Tare da amfani da wasu abubuwa ciki har da hotunan da ya samu daga hukumar tsaftar muhalli, Abubakar ya fara wayar da kan makwabtansa kan tsaftar muhalli.
Ya kuma taimaka wajen tara kuɗi don saye tare da gina masai a ƙauyen.
Wata da ke zaune a ƙauyen mai suna Hindatu Umar ta ce haƙiƙa gangamin na Abubakar ya kawo gagarumin sauyi a ƙauyen nasu.
Ta ce : “Maganar gaskiya, mun samu ci gaba. Gangamin na da matuƙar muhimmanci, saboda a yanzu ƙauyen ya tsaftata.
“Muna murna da wannan ci gaba. Mun samu gagarumin ci gaba a wannan fanni. A yanzu ba a ba-haya a fili. Mun kuma tsaftace ƙauyenmu.”

Ita ma a nata ɓangare Hauwa Umar ta ce “A yanzu, idan yaranmu suka yi amfani da masai, sukan wanke hannayensu, kai har ma manyan, suna amfani da masan yadda ya dace.''.
“Muna jin daɗin abin da wannan mutumin ke yi, kuma muna yaba masa.”
Abubakar na ƙoƙarin ganin ƙauyensa ya tsaftata, inda yake tabbatar da cewa mutane ba sa ba-haya a fili.
“Daga lokacin da na fara gangamin, mutane sun daina ba-haya a fili,” in ji shi. “Na tabbata da za ka zaga ƙauyen nan, za ka tabbatar da abin da nake faɗa.”
Yana kuma fatan yara masu tasowa za su ɗora a kan wannan gangami da ya faro.
Wayar da kan mutane kan batun na da matuƙar muhimmanci, tabbatar da tsaftar muhalli na da abu ne mihimmi.
“Akwai matasa da dama da za su ɗora daga inda na tsaya, ko da bayan na mutu, kuma na tabbata mutane za su saurare su.”
Wannan labari ya zo muku ne tare da tallafin Gidauniyar Bill & Melinda Gate Foundation
ncG1vNJzZmivp6x7o67CZ5qopV%2Bdrra%2FwGiYq6yZmLmmv46co7Btl2nHdMOTaqY%3D